Use APKPure App
Get Sheikh Aminu Daurawa - Manyan old version APK for Android
Wannan app yana dauke da wasu Manyan lekcoci masu fadakarwa daga Sheikh daurawa.
The app requires no internet connection to work (it is Offline) and voice quality is very high. Just download and start listening even when offline.
-------
Wannan app yana dauke da wasu zababun Manyan lekcoci masu fadakarwa daga Sheikh aminu ibrahim daurawa ke gabatarwa. Lectures din sune kamar haka:
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa - Harshenka Alkalinka Mp3
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa - Kaluben Matasa Mp3
Shine muka ga ya dace muyi application wanda mutane zasu su saurara a saukake.
Allah ya sakawa Sheikh ibrahim aminu daurawa domin yayi kokari wajen yayi kokari wajen yada ilimin Allah da na manzon sa domin karuwar al'umar musulmai. Mukuma Allah ya bamu ikon ji da kuma amfani daga abin da muka saurara.
Bayan bayani akan Harshenka Alkalinka Mp3 da kuma Kaluben Matasa Mp3, akwai lectures na Sheikh ibrahim aminu daurawa da kuma karatuttuka a cikin wannan manhaja idan akayi duba (wato in anyi sacin " rrnapps " a play store).
Akwai karatun malam Sheikh ibrahim aminu daurawa mp3 akan illar harshe, matsalolin aure by Sheikh ibrahim aminu daurawa mp3 dai sauransu.
za kuma a iya samun wasu karatuttukan na wasu malam irin su sheikh jafar mahmud adam, sheikh albani zariya, sheikh ali isah fantami, shiekh kabir gombe.
Za kuma a iya samun Karatun Al-quran na wasu daga cikin manyan makaranta quran.
Don Allah idan har kaji dadin wannan application a taimaka a yi sharing ta facebook, whatsapp, twitter, instagram da sauran social media domin sauran yan uwa musulmi su ma suyi downloading su amfana.
Kada kuma a manta ayi rating na wannnan application five star.
Kadan daga cikin tarihin Sheikh Ibrahim Aminu Daurawa,
TARIHIN SHEIKH AMINU DAURAWA KANO :-
Sunana Aminu Ibrahim bin Muhammad bin Bilal. Mahaifina shahararren malami ne, wanda ake kira Sheikh Ibrahim Muhammad mai tafsiri, gidan Zakara-Mai-Neman-Suna Fagge. Yana gabatar da tafisiri duk ranar Litinin da Alhamis, a unguwar Fagge, kusa da tsohuwar tashar kuka. Tsawon shekaru arba’in, kuma yana karantar da ilimi a zauren gidansa,
bayan kasuwanci da sana’ar dinki, domin dogaro da kai. Sunan mahaifiyata Hajiya Sa’adatu Al-Mustapha, daga unguwar Bachirawa, karamar hukumar Ungogo.
An haife ni a ranar 1 ga wata Janairu shekara ta 1969, a cikin garin Kano, a gida mai lamba 32 unguwar kofar Mazugal, a karamar hukumar Dala. Na fara karatun Alqur’ani mai girma tun ina dan karami, kuma na haddace shi a lokacin ina da shekara 14 zuwa 15. Bayan firamare da sakandare, da na yi, na kuma ci gaba da neman ilimi, domin fadada karatun addini, a wajen wadansu manyan mashahuran malamai na Kano: Wasu na Alqur’ani da tafsir, wasu na Alqur’ani zalla, wasu na ilimi da fannoninsa daban-daban. Wadannan manyan malamai su ne:
1. Alaramma Umaru Adakawa (Malam Tsoho) wanda na yi karatun Alqur’ani a wajensa.
2. Alaramma Salisu Bahadeje, layin tagwayen gida, wanda na yi karatun Alqur’ani a wajensa.
3. Alaramma Malam Na-Ande, makarantar Arzai, wanda na yi karatun Alqur’ani a wajensa.
4. Alhafiz Malam Abdullah Quru gwammaja.
5. Alaramma Malam Laminu Arzai, wanda na yi gyaran tilawa a wajensa.
6. Sheikh Auwal Isa ‘Yan Tandu, wanda na yi lugga da fiqihu da hadith a wajensa.
7. Sheikh Al-Mustapha Bazazzage layin tagwayen gida, wanda na yi lugga da fiqihu da tafsir a wajensa.
8. Sheikh Idi Kajjin ‘Yan Awaki, wanda na yi hadith da lugga a wajensa.
9. Sheikh Zakari Mai littafi, wanda na yi lugga da fiqihu a wajensa.
10. Sheikh Dogo Mai Mukhtasar Sabon Titi, wanda na yi nahawu da fiqihu a wajensa.
11. Sheikh Usman Gwammaja, layin azara, wanda na yi hadith da lugga da fiqihu da tarikh a wajensa. Wannan malami, na yi tsawon shekara ashirin ina karatun ilimi a wajensa. Allah ya ji qansa da rahama!
12. Sheikh Abubakar Basakkwace Qoqi, wanda na yi fiqihu da lugga a wajensa. Wannan malami, a wajensa na sauke Alfiyya din Malik, da Muqamatul Hariri, da Shu’ara’ul Jahiliyya. Malami ne mai haquri da juriyar karantarwa. da dai sauran malamai daban daban a duniya.
Mungode. Ayi saurare lafiya.
Last updated on Dec 8, 2020
*This Update includes bug fixes and improvements
Uploaded by
Mohammad Nassar
Requires Android
Android 4.1+
Category
Report
Sheikh Aminu Daurawa - Manyan
2.9 by engrshams
Dec 8, 2020